Sakamakon kira da ake yi ga daukacin Musulmi da su taimakawa wadanda harin bam ya shafa da su ke kwance a gadon asibiti. Hajiya Haliya Shekarau da ake yi wa lakabi da garkuwar Nakasassu ta kai musu dauki, inda ta yi musu goma ta arziki ta hanyar raba musu kudi har kimanin N10,000 kamar yadda za a iya gani a hoton.